Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi iya ƙoƙarinta wajen tallafa wa waɗanda hare-haren da suka faru a Jihar Filato suka shafa.
Tinubu ya yi wannan jawabi ne yayin da yake ganawa da iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a harin Jos a ranar Alhamis.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta bari irin wannan mummunan lamari ya sake faruwa ba.
A cewarsa:
“Ku shugabanni, na ji kukanku, kuma ga waɗanda abin ya shafa, babu abin da zan iya ba ku, ko da kuɗi ne masu yawa, sai dai in jajanta muku tare da yin alƙawarin cewa wannan abu ba zai sake faruwa ba.”
Ya kuma bayyana cewa dole ne ya gaggauta komawa saboda rashin hasken saukar jirgi a filin jirgin sama, amma ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.