Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Déby, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Taron ya samu halartar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Christopher Musa, tare da sauran manyan jami’an gwamnati.
Rahotanni sun ce an yi ganawar ne a kulle, inda shugabannin biyu suka tattauna kan muhimman batutuwa na bai ɗaya tare da duba hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa a yankin.
Ganawar ta gudana ne gabanin tafiyar Tinubu zuwa Jos domin jajanta wa waɗanda hare-haren baya-bayan nan a Jihar Filato suka shafa.
Ko da yake cikakken bayani bai fito ba, ana kyautata zaton tattaunawar na da alaƙa da ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannonin tsaro, kasuwanci da bunƙasa tattalin arziki.
Najeriya da Chadi na ci gaba da aiki tare a yankin Tafkin Chadi wajen magance matsalolin tsaro, ciki har da yaƙi da ta’addanci da barazanar ketare iyaka.