Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), António Guterres ya buƙaci a dakatar da yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran nan take.
Ya koka kan yadda yaƙin ya haifar da tashin farashin kayan masarufi da makamashi a duniya.
Guterres ya ce al’umma na shan wahala saboda yaƙin.
“Idan aka ci gaba da rufe mashigar Hormuz, masu ƙaramin ƙarfi ne za su sha wahala,” in ji shi.
Ya kuma yi kira da a samar da masalaha cikin ruwan sanyi, domin jin daɗin jama’a kuma a mutunta dokokin mallakar makamin nukiliya.
Ya ce: “Kira na ga Amurka da Isra’ila shi ne, su dakatar da yaƙin, saboda yana jefa al’umma cikin matsanancin hali’
“Ita kuma Iran, ta daina kai hare-hare kan maƙotanta”.