Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi gargadi ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) cewa ba za su iya tilasta ɗan takara ɗaya ga ‘yan Najeriya a zaben 2027 ba.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a asusun sa na X mai tabbaci.
Ya shawarci INEC da su bai wa ‘yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu cikin ‘yanci, ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka fito ba.
A cewar sa:
“Yau na haɗu da shugabannin African Democratic Congress (ADC) da sauran masu rajin dimokuradiyya a wani taron manema labarai na duniya domin sukar nuna bambancin ra’ayi da rashin adalci daga INEC.”
“Na goyi bayan matsayar taron: A 2027, dole ne a bai wa ‘yan Najeriya damar zaɓar shugabanninsu daga jam’iyyun siyasa daban-daban. Hukumar zaɓe ba ta da ikon tilasta ɗan takara ɗaya a mafi girman da kuma dimokuradiyyar Najeriya.”