Sarki Aminu Ado ya dakatar da hawan Sallah domin tabbatar da zaman lafiya a Kano

0 184

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da dakatar da shirin gudanar da hawan Sallah da aka tsara yi a birnin Kano yayin bukukuwan Babbar Sallah ta bana.

Sanarwar dakatarwar ta fito ne ta bakin Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, wanda ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da kuma karɓar shawarwari daga jami’an tsaro da hukumomin gwamnati.

A cewarsa, masarautar ta amince da dakatar da duk wasu shirye-shiryen hawan Sallah domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a faɗin Jihar Kano yayin gudanar da bukukuwan Eid-el-Kabir.

Ya ce masarautar tana bai wa zaman lafiyar al’umma muhimmanci fiye da komai, don haka ta ga ya dace ta bi shawarar hukumomin da ke da alhakin tabbatar da tsaro.

Tun da farko dai ana sa ran Sarkin Kano Aminu Ado Bayero zai gudanar da hawan Daushe tare da magoya bayansa a ranar Alhamis, kafin daga bisani a sanar da dakatar da shirin.

Masarautar ta kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.

Leave a Reply