Dalung Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Mayar Da Hankali Ga Siyasar 2027

0 158

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mayar da hankali kan siyasar zaɓen 2027 maimakon ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.

Dalung ya ce ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen dakile hare-haren ’yan bindiga, sace mutane domin neman kuɗin fansa da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a sassa daban-daban na Najeriya.

Ya bayyana cewa, a cewarsa, shagaltuwa da shirye-shiryen siyasar gaba tun yanzu na iya janye hankalin gwamnati daga muhimman batutuwan da suka shafi rayuwa da walwalar al’umma, musamman batun tsaro da tattalin arziki.

Tsohon ministan ya yi kira ga gwamnati da ta mayar da hankali kan tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, yana mai cewa hakan shi ne babban abin da al’umma ke sa ran gani daga shugabanni.

Leave a Reply