Dakarun Soja Na Operation Savannah Shield Sun Cafke Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai a Neja

0 178

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Savannah Shield sun kama mutane biyar da ake zargi da bai wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda bayanai a wasu hare-hare daban-daban da suka gudanar a Jihar Neja.

A wata sintiri da suka gudanar a yankin Doro da ke Wawa a Karamar Hukumar Borgu ranar 6 ga Yuni, 2026, dakarun sun cafke mutum uku da ake zargi da alaƙa da wata ƙungiyar ‘yan bindiga da ke aiki a yankin Duru da ke gefen dajin Kainji.

Binciken farko ya nuna cewa an kwato wayoyin Tecno biyu masu maɓalli, na’urar MP3 ɗauke da saƙonnin farfaganda da iƙirarin sace wani mutum a Jihar Kaduna tare da karɓar kuɗin fansa na Naira miliyan 60, da kuma kuɗi Naira 113,400.

Haka kuma, dakarun Bataliya ta 221 sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da aikin leƙen asiri a kusa da sansanin soji. Binciken wayar ɗaya daga cikinsu ya gano hoton wani mutum da aka kashe, wanda aka ɗauka tun ranar 2 ga Mayu, 2026, lamarin da ya ƙara nuna yiwuwar alaƙarsu da ayyukan ta’addanci.

An kuma kwato wayar Android guda ɗaya, wayar Tecno mai maɓalli, babur guda ɗaya da kuma kuɗi Naira 86,100 daga hannunsu.

Rundunar ta ce waɗannan nasarori sun nuna ƙudirin dakarun Operation Savannah Shield na tarwatsa hanyoyin tallafa wa ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka, tare da ci gaba da matsa lamba domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya.

Sanarwar ta fito ne daga Kyaftin Jamilu Muhammed Yahaya, Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Savannah Shield.

Leave a Reply