Jami’in ‘yan sanda ya nuna damuwa kan yadda ake lalata kayan makaranta a jihar Jigawa

0 186

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, SP Shi’isu Lawan Adam, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu suka lalata kayan wata makarantar firamare da ke garinsu tare da sayar da su a kan kuɗi kaɗan.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce abin takaici ne yadda aka cire kwanukan aluminium na azuzuwa tare da kakkarya benci da kujeru aka sayar da su, ba tare da wani daga cikin al’ummar yankin ya lura ko ya dakatar da lamarin ba.

Ya bayyana cewa irin wannan ɗabi’a na nuna rashin kishin al’umma, yana mai tambayar ko za a kira abin jahilci, mugunta, wauta ko kuma dabbanci.

Leave a Reply