Tsohuwar Minista Sadiya Farouq Ta Nemi Kotu Ta Soke Sammacin Kama Ta

0 163

Tsohuwar Ministar Harkokin Jin-ƙai, Sadiya Umar Farouq, ta roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta soke sammacin kama da aka bayar a kanta kan zargin da ake yi mata tare da wasu tsofaffin jami’an ma’aikatar.

A zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin, Farouq ba ta halarta ba, inda lauyanta ya bayyana cewa tana fama da rashin lafiya. Sai dai lauyan Hukumar EFCC ya nuna adawa da sauraron buƙatar, yana mai cewa bai kamata a yi hakan ba kafin a gurfanar da ita a gaban kotu.

Lauyan Farouq ya dage cewa kotun na da ikon sauraron ƙorafin da ta shigar, wanda ke neman a soke sammacin kama da Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya bayar tun ranar 16 ga Afrilu.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Onwuegbuzie ya ɗage shari’ar zuwa ranar 10 ga Yuni domin yanke hukunci kan buƙatar da tsohuwar ministar ta gabatar.

Leave a Reply