Akalla mutane biyu aka kashe wasu kuma suka jikkata bayan fadan makiyaya da manoma a kamaramar hukumar Minjibi da ke kano
Kimanin kauyuka 10 rikicin ya rutsa dasu tare da lalata amfanin gona mai yawa
Shedun gani da ido sunce al’amarin ya faru a karshen mako yayin da makiya suka saki dabobin su zuwa gonakin da aka girbe
Manema labarai sun rawaito cewa kauyukan Daurawa, Kuka Bakwai, Geza, Macinawa da Kasakore naga cikin garuruwan da rikicin yafi kamari
Guda daga cikin mazauna yankunan Basiru Dauda Kunya, yace maharan sun takurawa yankunan tun shekarar data gabata wannan yasa mutane suka dauki mataki a wannan makon
Sai dai kuma a cewar shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah yace rikicin ya faru ne sakamakon manoman sunyi shuka a wuraran kiwo
Kakakin yan sandar Jahar Sp Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace komai ya dai-daita yanzu haka