An kashe mutane biyu wasu kuma suka jikkata bayan fadan makiyaya da manoma a karamar hukumar Minjibir dake kano

0 94

Akalla mutane biyu aka kashe wasu kuma suka jikkata bayan fadan makiyaya da manoma a kamaramar hukumar Minjibi da ke kano

Kimanin kauyuka 10 rikicin ya rutsa dasu tare da lalata amfanin gona mai yawa

Shedun gani da ido sunce al’amarin ya faru a karshen mako yayin da makiya suka saki dabobin su zuwa gonakin da aka girbe

Manema labarai sun rawaito cewa kauyukan Daurawa, Kuka Bakwai, Geza, Macinawa da Kasakore naga cikin garuruwan da rikicin yafi kamari

Guda daga cikin mazauna yankunan Basiru Dauda Kunya, yace maharan sun takurawa yankunan tun shekarar data gabata wannan yasa mutane suka dauki mataki a wannan makon

Sai dai kuma a cewar shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah yace rikicin ya faru ne sakamakon manoman sunyi shuka  a wuraran kiwo

Kakakin yan sandar Jahar Sp Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace komai ya dai-daita yanzu haka

Leave a Reply

%d bloggers like this: