Home Articles posted by Sawaba FM
Labarai

Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a kasarnan ta hanyar zuba jari a bangarori masu muhimmanci cikin shekaru bakwai da suka gabata. Ya fadi haka cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a jiya domin taya yaran Najeriya murnar bikin ranar […]Continue reading
Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami musamman a lokacin gudanar da zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam da ya rabawa manema labarai […]Continue reading
Labarai

Jarirai 11 sabbin haihuwa sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani asibiti a birnin Tivaouane da ke yammacin kasar Senegal

Jarirai 11 sabbin haihuwa sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani asibiti a birnin Tivaouane da ke yammacin kasar Senegal. Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce gobarar ta tashi a sashen haihuwa na asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh. A cewar ‘yan siyasar Senegal, rahotannin farko sun nuna cewa gobarar ta […]Continue reading
Labarai

Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta aurar da wasu mata da suka musulunta inda ta dauki nauyin aurensu

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta aurar da wasu mata da suka musulunta, inda ta dauki nauyin aurensu; da saya musu gadajensu da sauran kayan daki da kayan kicin. Daraktan gudanarwa na hukumar, Auwal Lamido, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa yau a Kano cewa hukumar ta kuma warware wasu kararraki bakwai […]Continue reading
Labarai

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja. Shugaban kwamitin zaben Lawrence Ewhrudjakpo ne ya sanar da hakan a sakateriyar jam’iyyar PDP ta jihar, wajen da ake gudanar da zaben fidda gwani a Minna babban birnin jihar.. An ce an kashe wakilan […]Continue reading
Labarai

Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal

Wasu ‘yan takarar gwamna biyu na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa, sun yi watsi da zaman ganawar da gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ya kira domin a samar da dan takarar guda ta hanyar sulhu a jihar. Ba a cimma matsaya a zaman ganawar ba. Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya kira zaman […]Continue reading