Man fetur din Dangote zai fara shiga kasuwa a ranar 15 ga watan nan

0 98

Kamfanin man fetur na kasa NNPCL tace man fetur samfurin matatar man fetur ta Dangote zai soma shiga kasuwa a ranar 15 ga watan satumbar nan.

Kamfanin ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban jami’in sadarwa Olufemi Soneye a jiya Alhamis a Abuja yace kasuwa ce zata yiwa man fetur din farashi.

Cigaban ya biyo bayan sanarwar matatar na soma tace man a farkon makon nan.

A hannu guda Gwamnatin tarayya tace ta bai wa ƴan jama’a tabbacin gushewar ƙarancin man fetur ɗin da ake fuskanta nan gaba kaɗan, sai dai ta ce ba ta da yadda za ta yi game da tashin farashin man da ake gani a sassan ƙasa, domin ba ita ke da hurumin ƙarawa ko rage farashin ba.

Kamar yadda Ƙaramin ministan man fetur na kasa Sanata Heineken Lokpobiri ya bayyana a jawabinsa gaban taron manema labarai bayan wata ganawa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: