Shugaban kasa Bola Tinubu yace kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta himmatu matuka gaya wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci da magance matsalolin tsaro.
Ya bayyana hakan ne a Birnin Beijing na kasar China, lokacin da yake jawabi a wani taron shugabanni kan zaman lafiya da tsaro na bana da hadin kai tsakanin kasashen Afrika da China.
Tinubu yace a Najeriya gwamnatin sa ta mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakanin kashen yammacin Afrika.
Ya kuma yabawa tallafin kasar China wajen bunkasa cigaban nahiyar Afrika.
Tinubu ya kuma bayyana muhimmancin aukawar matsalolin tsaro tun daga tushe, kamar talauci, rashin dai-daito, da rashin adalcin zamantakewa, yana mai cewa matukar za’a kawo sauyi, ya zama wajibi, a samar da adalci, daidaito, samar da damarmakin tatalin arziki da bunkasa tsaron dan adam.