Sheikh Bashar Danfili ya kokan kan yadda yan bindiga ke ciyar da karnukansu naman mutane

0 109

Wani Shahararren malamin addinin musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Bashar Danfili, ya kokan kan yadda yace yan bindiga a jihar sun soma ciyar da karnukansu naman mutane, daga cikin wadanda sukayi garkuwa dasu.

Shekin malamain ya bayyana haka ne lokacin da yake neman taimakon jama’a da kudi bayan wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan uwansa guda shida a hanyarsu ta zuwa wani kauye a jihar.

A cikin wani gajeren faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta, malamin ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da wani mutum, mahaifiyarsa, matar mahaifinsa, matan sa biyu da kuma kanwarsa.

Ya ce ‘yan fashin sun bukaci makudan kudade da ba za su iya tarawa ba, ya kara da cewa wa’adin yana kara kusantowa.

Danfili ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da ‘yan uwansa na kusa, inda nan take aka kashe direbansu, sannan ‘yan bindigar sun ciyar da karnukan su naman gawar direban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: