Mayaƙan Lakurawa sun kashe jami’an kwastam biyu a Kebbi

0 65

Wasu mayaƙan ƙungiyar Lakurawa sun kashe jami’an kwastam biyu yayin harin da suka kai kan shingayen tsaro a ƙaramar hukumar Bagudu da ke Jihar Kebbi.

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adeniyi, ya ce an harbe jami’i guda yayin da aka kona wani babban jami’i da rai a lokacin artabun.

Ya bayyana cewa jami’an da suka rasu sun haɗa da mataimakin sufaritanda Bamigboye da jami’i mai suna Dom.

Shugaban kwastam ɗin ya ce rasuwar tasu abin takaici ne, amma hakan ba zai hana jami’an tsaro ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka a iyakokin ƙasar ba.

Leave a Reply