Ƴansanda sun kama mutum mai shekara 60 kan zargin yi wa yarinya fyade a Bauchi

0 238

Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekara 60 mai suna Musa Garba bisa zargin lalata da wata yarinya mai shekara tara a yankin Magama Gumau da ke ƙaramar hukumar Toro.

Kakakin rundunar, CSP Nafiu Habib, ya ce mahaifin yarinyar ne ya kai rahoton lamarin ga ƴansanda bayan zargin cewa mutumin ya yaudari yarinyar zuwa wani wuri a ranar 7 ga Mayu, 2026.

Ƴansanda sun bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin yayin bincike, tare da cewa ya aikata irin hakan a lokuta daban-daban.

Har ila yau, yarinyar ta ambaci wani mutum mai suna Nafi’u da ake zargi da hannu a makamancin lamarin, wanda a yanzu haka ya tsere, yayin da bincike ke ci gaba.

Leave a Reply