Majalissar Dattijai ta ware naira miliyan 200 ga kowanne sanata domin gudanar da ayyukan mazabu a kasafin kudin 2024

0 313

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Ali Ndume, ya ce an ware naira miliyan 200 ga kowanne sanata a zauren majalissar Dattijai ta 10 domin gudanar da ayyukan mazabu a kasafin kudin 2024.


Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba, Ndume ya ce Sanatoci 10, wadanda su ne shugabanni, ciki har da shi kansa, sun samu sama da Naira miliyan 200.
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka yi ta sabata juyatta tare da cece-kuce game da kasafin kudin shekarar 2024 a sakamakon zargin da ake yi na cushe da kuma shigar da ayyuka a ciki.


A ranar Asabar din da ta gabata ne Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi ya tayar da kura a lokacin da ya yi zargin cewa majalisar ta yi aringizon kasafin kudi har naira tiriliyan uku.
Zargin da ya janyo cece-kuce a zauren majalisar dokokin saboda da yawa daga cikin sanatoci sun fusata kan ikirarin Ningi.


A yayin muhawarar, dan majalisa mai wakiltar Cross River ta arewa, Jarigbe Jarigbe, ya yi ikirarin cewa wasu “manyan sanatoci” sun samu Naira miliyan 500 a cikin kasafin kudin 2024 na ayyukan mazabu.
Daga bisani dai, an dakatar da Ningi na tsawon watanni uku.


Da yake magana game da lamarin, Ndume ya ce Ningi bai yi kuskure ba game da zargin kashe kudi. Saidai ya ce Sanatan na Bauchi yana son mayar da kasafin kudin 2024 batun kabilanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: