Mutum takwas sun mutu a hatsarin mota a jihar Kogi

0 166

Mutum takwas ne suka rasa ransu a wani hatsarin mota a yankin Aloma a karamar hukumar Ofu na jihar Kogi.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kogi Samuel Oyedeji ya tabbatar da faruwar lamarin a Lokoja, babban birnin jihar.

Ya ce hatsarin ya afku ne ranar Lahadi kuma ya shafi fasinjoji 21.

Oyedeji ya ce wasu mutum 13 kuma sun samu raunuka daban-daban a gobarar da ta tashi sakamakon hatsarin.

Wani ganau ya faɗa wa gidan talabijin na Channels cewa wata motar Sienna ce da ke hanyar zuwa Abuja daga Fatakwal, ta yi taho-mu-gama da motar bas, abin da ya janyo tashin gobara da kuma ya yi sanadiyar mutuwar wasu fasinjoji.

Ganau ɗin ya ɗora laifin afkuwar hatsarin kan gudu fiye da kima da kuma rashin kyawun hanya, inda ya ce sun shafe sa’o’i uku kafin su sami damar cire direban ɗaya daga cikin motocin daga motarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: