Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ya gayyaci Ministan Lantarki na kasa

0 152

Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ya gayyaci ministan lantarki na kasa, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar NERC da su bayyana a gabansa  wani zaman bincike da za a yi game da ƙarin kuɗin lantarkin da aka yi a baya-bayan nan.

Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ne ya bayyana haka yayin gudanar da ayyukan kwamitin da kuma kai ziyara zuwa ma’aikatar lantarki da ke Abuja.

Abaribe ya ce majalisar dattawa tuni ta amince a yi zaman ranar 29 ga watan Afrilu inda hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi.

Ministan ya bayyana tarin matsalolin da suka addabi ɓangaren lantarki a Najeriya da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da rashin iskar gas inda ya buƙaci kwamitin da ya tallafa wa ma’aikatar lantarki domin cimma ƙudurorinta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: