Aisha Muhammad Lawan
Kwamishinan ma’aikatar Ilmi mai zurfi na jihar Jigawa, Dr Isa Yusif Chamo ya bada umarnin dakatar da Daraktan kwalejin Birnin Kudu da kuma jami’in kula da harkokin abinchi na kwalejin wato kitchen master ba tare da bata lokaci ba.
Kwamishinan ya bada umarnin ne a wata ziyarar bazata da ya kai kwalejin, inda yace ya ziyarci kwalejin ne domin ganin yadda ake ciyar da dalibai bisa sabon tsarin gwamnatin jihar.
Ya nuna rashin jin dadinsa bisa irin yanayin abinchin da ya gani a kwalejin duk kuwa da Karin kudaden ciyarwa da gwamnatin jiha tayi da kaso hamsin cikin dari.
Dr Isa Yusif Chamo yana mai cewar zai cigaba da rangadin makarantun kwana domin ganin yadda ake ciyar da dalibai, kuma duk shugaban da aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.
Kwamishinan ya kuma umarci Dakataccen Daraktan kwalejin na Birnin Kudu da ya kai kansa da kansa maaikatar Ilmi mai zurfi ta jiha yayinda shi kuma dakataccen jamiin kula da abinchi na kwalejin da ya kai kansa da kansa ofishin shiyyar Ilmi ta Birnin Kudu.
Dr Isa Yusif Chamo ya kuma umarci mataimakin Daraktan kwalejin Salisu Haruna Majia da ya kula da kwalejin yayinda ya umarci senior master na kwalejin Yahaya Ibrahim ya zama jamiin kula da harkokin abinchi wato kitchn master na kwalejin.