Gwamna Dikko Radda ya kare ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai kasar Amurka

0 90

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya ce sun yi hakan ne domin nemo mafita mai dorewa kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Gwamnonin dai sun sha suka kan ziyarar da suka kai Amurka.
Sai dai Radda ya ce ziyarar wani bangare ne na daukar matakan magance matsalar tsaro a arewacin kasa, inda ya bayyana cewa an gayyace su ne taron.
Duk da sukar da ake yi kan taron tare da tambayar dalilin da ya sa aka gudanar da taron a Amurka ba a Najeriya ba, Radda ya kare tafiyar.
A cewar Radda, ziyarar ta Amurka ta baiwa gwamnonin damar fahimtar kalubalen tsaro da ke addabar yankin arewa.
A shekarun baya-bayan nan dai yankin arewa yana fama da matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma matsalolin tsaro da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: