Gwamnan Jihar Gombe ya yi kira ga sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi da su yi aiki tukuru

0 86

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kira ga sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi 11 da mataimakansu da kansiloli 114 da su yi aiki tukuru domin ci gaban yankunansu, inda ya taya su murnar lashe zabe.
Ya kuma bukaci da su dauki zaben nasu a matsayin wani nauyi na yi wa jama’a hi-dima a irin wannan lokaci mai matukar muhimmanci.
Gwamnan a wata sanarwa da ya fitar dauke da sanya hannun hadiminsa, Ismaila Uba Misilli, biyo bayan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Gombe ta fitar, ya taya jam’iyyar APC mai mulki murnar samun gagarumar nasara a zaben.
Ya bayyana jin dadinsa da yadda zaben ya gudana ba tare da tangarda ba.
Gwamnan ya kuma yabawa hukumar zaben da jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi wajen ganin an gudanar da zaben cikin sauki, wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: