Gwamna Namadi yayi kira ga sabbin masu yiwa kasa hidima da aka turo jihar jigawa da su kasance jakadu na gari

0 204

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi yayi kira ga sabbin masu yiwa kasa hidima da aka turo jihar jigawa da su kasance jakadu na gari da kuma bin dokoki a lokacin zamansu.

Gwamnan ya bayyana haka ne alokacin bikin rantsar da masu yiwa kasa hidima kashi na biyu a sansaninsu dake Fanisau.

Gwamnan wanda Mataimakinsa Injiniya Aminu Usman Gumel ya wakilta ya bayyana haka ne lokacin bikin rantsar da masu yiwa kasa hidima rukunin A, kashi na biyu da aka gudanar a Fanisau dake Birnin Dutse.

Yace jihar jigawa, jiha ce mai zaman lafiya, tare da mutunta baki, saboda haka akwai bukatar su kasance masu tarbiyya da kuma bin ka’idoji alokacin zamansu a jihar.

Daga nan ya ja hankalinsu dasu kasance masu koyon sana’o’in dogaro da kai da kuma harkokin koyo da koyarwa, inda ya bada tabbacin goyon bayan gwamnatin jiha domin samun nasarar da ake bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: