Shugaba Bola Tinubu ya amince da wasu tsare-tsare guda uku don inganta fannin ilimi a kasar nan

0 231

Tsarin zai yi wa fannin ilimi gabaki daya garambawul don inganta koyo da bunkasa fasaha, da kara yawan shigar da yara da kuma tabbatar da tsaro.

Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis a Abuja.

Mista Ngelale ya ce hakan zai kunshi bayanai kan dukkan makarantu tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu, wanda ya kunshi wuraren zamansu, da  kayan koyo da koyarwa da dai sauransu. Ngelale ya ce bayanan za su jagoranci ayyukan gwamnatin tarayya da na jihohi don horar da malamai da ci gabansu da kuma bayar da tallafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: