Rundunar sojin Najeriya ba za ta tsagaita ba wajen kawar da masu aikata miyagun laifuka

0 107

Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ce rundunar sojin Najeriya ba za ta tsagaita ba wajen kawar da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka da ke haifar da kalubale na rashin tsaro a kasar nan.

Ya kuma umurci kwamandoji a kowane mataki da su kasance masu hazaka da jajircewadomin yakar abokan gaba masu gurbata yananin tsaron kasar nan. Da yake jawabi a wajen rufe taron hafsoshin tsaron kasa a Abuja, Lagbaja ya tabbatar wa ‘yan Najeriya aniyar rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: