Tinubu ya nuna rashin jindadinsa kan mafi karacin albashi na Naira 615,000

0 135

Shugaba Bola Tinubu ya nuna rashin jindadinsa kan mafi karacin albashi na Naira 615,000, ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya na bana a Abuja.

Haka kuma, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, a wata hira da ya yi da manema labarai ya caccaki ma’aikata kan nacewar Naira 615,000 kan mafi karancin albashi. Ya ce gwamnati da kungiyoyin kwadago ba su amince da adadin mafi karancin albashi ba.

Sai dai shugaban kungiyar kwadago na kasa, Joe Ajaero, ya kare bukatar ma’aikata, yana mai jaddada cewa kungiyar ba za ta amince da duk wani kudi da zai talauta mambobinta ba. Ya kuma ce kungiyoyin kwadagon sun amince da Naira 615,000 a matsayin albashin ma’aikatan gwamnati.

Gwamnati ta gaza bayyana sabon mafi karancin albashi a bikin ranar Ma,aikiata ranar Laraba saboda ba ta amince da bukatar kwadago ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: