Gwamnatin tarayyar ta tsara shirin samar wutar lantarki mai dorewa ga Najeriya

0 156

Gwamnatin tarayyar ta tsara shirin samar da megawatts 10,000 ta hanyar samar da wutar lantarki mai dorewa ga Najeriya tare da hadin gwiwar bankin duniya.

Babban makasudin aikin shi ne haɓaka amfani da wuraren ajiya da ake da su don samar da ruwa da wutar lantarki. 

Hakan dai yana  nufin ƙarfafa tsare-tsare da hukumomi masu zuba jari sarrafa albarkatun ruwan da Najeriya ke dasu.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a yayin taron koli na babban kan makamashi mai dorewa a cikin hadin gwiwar da aka sabunta a  karni na 21, wanda aka gudanar jiya Laraba a Abuja .

Adelabu ya jaddada arzikin da Najeriya ke da shi na albarkatun ruwan da ake dasu a fadin kasar nan. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: