Majalisar dattijai ta amince da bukatar Shugaba Tinubu na ciyo bashin Dala Miliyan 500

0 147

Majalisar dattijai ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na ciyo bashin  Dala Miliyan 500 ga Hukumar Kamfanonin Jama’a (BPE) don inganta harkokin kudi da fasaha na kamfanonin rarraba wutar lantarki, da nufin amfanar ‘yan kasa.

Amincewar ya biyo bayan nazarin rahoton Sanata Aliyu Wamakko wanda ya jagoranci kwamitin majalisar dattijai mai kula da basussukan cikin gida da waje na 2022 – 2024 a ranar Talata.

Bashin Dalar Amurka Miliyan 500 na daga cikin bashin Dala Biliyan 7.94 wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa a ranar 1 ga watan Nuwamba 2023 karkashin shirin 2022-2024 na karbar bashin kasashen waje da kuma neman amincewar bashin Yuro Miliyan 100.

Sai dai majalisar dattijan ta amince da ciyo bashin Dala Biliyan 7.4 a zamanta na a ranar 30 ga watan Disamba bayan nazarin rahoton kwamiti kan basussukan cikin gida da na waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: