A ranar Larabar da ta gabata ne wasu dalibai biyu na kwalejin koyon aikin gona ta Audu Bako da ke Makoda suka nutse a dam din Thomas da ke jihar Kano a lokacin da suke kokarin tsallakawa a cikin jirgin ruwa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce wadanda suka mutu sun hada da Abubakar Sanusi mai shekaru 22 da Salisu Ado mai shekaru 21.
An ceto abokin aikinsu na uku Ibrahim mai shekaru 21, kuma a halin yanzu yana samun kulawar likitoci a babban asibitin Dambatta.