Jami’an ‘yan sanda a Katsina sun dakile wani hari da aka kai garin Sabuwa dake jihar

0 93

Jami’an ‘yan sanda a Katsina sun dakile wani hari da aka kai garin Sabuwa, dake jihar, inda suka kashe wani da ake zargin dan fashi ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Alhamis a Katsina.

Ya ce, a ranar 17 ga Afrilu, 2024, da misalin karfe 5 na yamma, an samu labarin cewa wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a adadinsu, dauke da muggan makamai irin su AK-47, a kan babura, suna kan hanyar zuwa garin Sabuwa da nufin kai hari.

Hukumar ta hannun jami’in hulda da jama’ar ta, ta bayyana cewa, a yayin da ake duba wurin, an gano gawar wani dan bindiga da aka kashe. Ya kara da cewa, an kuma samu nasarar gano wani abin fashewa a inda lamarin ya faru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: