An shawarci al’ummar jihar Jigawa su tashi tsaye wajen dasa bishiyoyi da renon su

0 116

An shawarci al’ummar Jihar Jigawa su tashi tsaye wajen dasa bishiyoyi da renon su har su girma domin kare gurbatar muhalli da kuma sauyin yanayi.

Shawarar ta fito ne daga bakin, Malam Na’allah Dutse wanda ya na daya daga cikin mahalarta bitar yini biyu da hukumar kula da dashe da kuma renon bishiyoyi na ma’aikatar kula da muhalli ta tarayya ta shiryawa yan kungiyoyin da suka fito daga jihohin arewa maso gabas da aka gudanar a birnin Kano.

Malam Na’allah Dutse ya ce an shirya taron bitar ne domin fadakar da al’umma illar dimama da kuma sauyin yanayi da ake fuskanta a halin yanzu.

Ya ce wadanda suka shirya bitar sun bukaci mahalarta bitar dasu dawo jihohin su domin wayar da kan al’umma dangane da illar dimama da kuma sauyin yanayi ga gonaki da dabbobi da kuma bil-adama.

Haka kuma Malam Na’allah Dutse ya kara da cewa wannan bita na daya daga kudirorin Gwamna, Malam Umar Namadi goma sha biyu na bunkasa aikin gona da kuma kare muhalli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: