Ministan ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ya kaddamar da cibiyar samar da ruwan sha dake garin Birnin Kudu

0 167

Ministan ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na tarayya Injiniya Joseph Utsev ya kaddamar da cibiyar samar da ruwan sha dake garin Birnin Kudu.

A jawabin da ya gabatar Ministan, yace ma’aikatar ta kaddamar da irin wadannan ayyuka a jihohin Kano da Jigawa domin samarwa al’umma isashen ruwa sha. 

Injiniya Joseph Utsev ya ce gwamnatin tarraya zata cigaba da samarwa al’umma ruwan sha mai tsafta a fadin kasar nan.

Ya bayyana cewa ma’aikatar tuni ta dukufa wajan wayar da kan jama’a illar yin bahaya a bainar jama’a domin samun tsaftatcen muhalli.

A nasa jawabi Manajan Darktan hukumar bunkasa kogunan Hadejia/Jama’are Alhaji Ma’amun Da’u Aliyu ya ce hukumar tayi la’akari da mawuyacin halin da karancin ruwa da garin birnin kudu yake ciki, don haka hukumar ta samar da tankin bada ruwan sha daban-daban masu cin lita dubu uku-uku a ungwannin masamawa da Dutsin Maidodo da cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da kuma kwalejin birnin Kudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: