Tun da Na Zama Gwamnan Kaduna Ban Karɓi Bashin Sisin Kobo Ba – Uba Sani

0 29

Tun da na zama gwamnan Kaduna ban karɓi bashin sisin kobo ba – Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ba ta karɓi wani sabon bashi ba tun bayan da ya hau mulki a 2023, duk da cewa tana ci gaba da biyan bashin da ta gada daga gwamnatocin baya.

Uba Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels TV a ranar Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda gwamnatinsa ke kashe kuɗaɗe da kuma ƙarin kuɗaɗen shiga da jihar ke samu.

A cewar gwamnan, a halin yanzu Jihar Kaduna tana ware kimanin naira biliyan 6.7 a kowane wata domin biyan bashin da ta gada daga gwamnatocin da suka gabata.

“Tun da na zama gwamna, ban karɓi koda kwabo ɗaya na bashi ba,” in ji gwamnan.

Ya danganta wannan mataki da abin da ya bayyana a matsayin tsantsar kula da harkokin kuɗi cikin hikima da kuma yin taka-tsantsan wajen tsara abubuwan da gwamnati za ta kashe kuɗinta a kansu.

“Batu ne na yin taka-tsantsan da yin abin da ya kamata, da kuma ta zaɓar wuraren da suka dace a zuba jari cikin kulawa sosai,” in ji shi.

Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori masu yawa, yana mai nuni da ci gaban da aka samu a fannonin noma da ilimi da bunƙasa sana’o’i da kuma tsaro.

Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin arewacin ƙasar da ke fuskantar matsalolin tsaro, musamman yanbindiga masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply