Kasafin kudin Jihar Jigawa na shekarar 2023 ya kai Naira Biliyan 178 da Miliyan 500

0 85

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya gabatar da kasafin kudin Jihar Jigawa na shekarar 2023, na Naira Biliyan 178 da Miliyan 500 ga Zauren Majalisar Dokokin Jihar a jiya Laraba.

Gwamnan ya ce kasafin kudin ya rabu biyu ta fuskar manyan ayyukan wanda zasu cinye kaso 50 na kasafin kudin da kuma bunkasa fannin kasuwanci.

Kasafin kudin ya kunshi Naira Biliyan 61 da Miliyan 200 wanda aka warewa fannin Ilimi da kuma Naira Biliyan 28 da Miliyan 900 domin fannin Lafiya.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira Biliyan 89 da Miliyan 400 domin gudanar da manyan ayyuka. Sannan an ware Naira Biliyan 14 da Miliyan 42 domin kammala wasu ayyukan a fannin Lafiya wanda ake gudanarwa yanzu a haka.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Hon Garba Jahun, ya yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa yadda ya samar da cigaba a fannin Noma, kasuwanci da kuma abubuwan more rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: