Kungiyar NULGE reshen karamar Hukumar Buji ta yabawa wakilin mazabar Buji a majalisar dokoki

0 84

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa reshen karamar Hukumar Buji ta yabawa wakilin mazabar Buji a majalisar dokokin jiha Sale Baba Buji bisa gudanar da aiyyukan raya kasa a fadin yankin

Shugaban kungiyar Comrade Saleh Abdullahi Gantsa ne ya bayyana haka a lokachin da suka ziyarci dan majalisar a ofishinsa. 

Comrade Saleh Gantsa yace dan majalisar yana kokari wajan gudanar da ayyukan mazabu a bangarorin samar da ruwansha da gina masallatan Juma’a dana kamsa salawati, tare da tallafawa mararsa lafiya

Da yake maida jawabi, Honourable Sale Baba Buji yace aiyukan dan majalissa sun hadar dayin doka da kuma samarwa da alumma kayayyakin more rayuwa da gwamna Umar Namadi ya sahalewa yan majalissar dokokin jiha. 

Honourable Sale Baba yace zai bar kofarsa a bude domin karbar shawarwari da zasu ciyar da karamar hukumar gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: