Hukumomi sun kwashe kusan mutane dubu 60 daga gidajensu da ke Guangdong yayin da mamakon ruwan saman da aka shafe kwanaki ana yi ya janyo ambaliyar ruwa a lardin da ke da mafiya yawan al’umma a China.
Mutane 11 ne suka yi ɓatan dabo sai dai ba a bayar da rahoton asarar rai ba.
Wani Bidiyo daga kafafen yaɗa labaran ƙasar sun nuna yadda ambaliyar ruwan ta shafe wurare inda kuma masu aikin ceto cikin kwale-kwale ke kwashe mutane daga ruwan da tsayinsa ya kai ƙugunsu.
Manyan kogunan ƙasar sun tumbatsa sannan hukumomi suna sa ido kan lamarin.
A sassan lardin, kusan gidaje miliyan 1.16 sun faɗa cikin duhu a karshen mako amma an gyara wutar kashi 80 cikin 100 na gidajen a jiya Lahadi da daddare.
An soke tashin jirage, wasu kuma an jinkirta lokacin tashin su a filin jirgin saman Baiyun da ke Guangzhou saboda ruwan daka ayi ta zabgawa yayin da kuma aka buƙaci makarantu a birane aƙalla uku da su rufe.