Babban Sufeto Janar na Yan sandan Usman Alkali ya gabatar da chekin kudi sama da Naira miliyan 22 ga iyalan jami’an Yan sanda da suka mutu a jihar Filato.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Jos.
Alkali wanda kwamishinan Yan sandan jihar Filato Bartholomew Onyeka ya wakilta ya gabatar da cakin.
Sufeto-janar na ‘yan sandan ya ce hakan na goyon bayan iyalan ’yan sandan da suka mutu a bakin aiki, yana mai cewa hakan zai ba su damar samun abin dogaro da kai.
Nankin Njin, wanda ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya godewa sufeto-janar na ‘yan sandan bisa wannan karamcin tare da bayar da tabbacin cewa za a yi amfani da su sosai.