Cutar kwalara tayi ajalin mutum 169 a Kano, 191 a kwance a asibiti

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ɓarkewar cutar kwalara a kananan hukumomin ta guda 44 na jihar ya yi ajalin mutane 169, yayinda 191 ke kwance a asibiti a halin yanzu.

Kamar yadda BBCHausa ta ruwaito, Darakta a fanin lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiyar jihar, Dr Ashiru Rajab ya shaida cewa an tattaro waɗanan alkaluma ne a cikin watannin uku, sannan ya ƙara da cewa mutum 5,221 suka kamu da cutar, cikinsu 4,860 sun samu sauki kawo yanzu.

Saidai a cewarsa, mutum 191 da ke kwance yanzu a asibiti na samun kulawa a asibitocin gwamnati dake wadannan kananan hukumomin.

Dr Rajab ya yi kira ga al’umma da su kula da tsafta da abubuwan da suke ci, musamman mazauna karkara domin kare kai.

Comments (0)
Add Comment