Dakarun sojojin Najeriya sun ce mayaƙan ISWAP da iyalansu fiye da 100 sun yi saranda

Dakarun ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP) da iyalansu 104 sun miƙa wuya ga sojojin Najeriya, a cewar rundunar sojan ƙasar.

Wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na zumunta, rundunar ta ce mayaƙan da suka yi saranda a ranar Asabar sun ƙunshi maza 22 da mata 27 da yara 55.

Ta ƙara da cewa sun kai kan su ne ga dakarun rundunar musamman ta 25 da ke Damboa a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Yaƙin Boko Haram ya yi sanadiyyar kisan mutum aƙalla 300,000 sannan ya raba fiye da miliyan 2.5 da muhallansu, a cewar alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Comments (0)
Add Comment