Tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya mika ragamar mulki ga sabon kwamitin gudanarwar jam’iyyar (NWC) karkashin jagorancin Tanimu Turaki.
Wa’adin kwamitin Damagum zai kare ne a ranar 8 ga Disamba, 2025, bayan wani rikicin shugabanci tsakaninsa da bangaren da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ke mara wa baya.
An gudanar da bikin mika mulkin ne a Gidan Gwamnan Bauchi da ke Abuja.
Da yake jawabi, Damagum ya ce sabon NWC ya samu cikakkiyar dama da daukar nauyin farfado da hadin kan PDP. Ya ce:
“Abin alfahari shi ne mun sha wahalhalu sosai, amma mun tsallake su, kuma za mu ci gaba da tsallake kowace barazana”.
Damagum ya kara da cewa makomar PDP akwai haske a gaba, sannan har yanzu ita ce jam’iyyar da ake tsoro a fafutukar siyasa a Najeriya.
“Shi ya sa suke kasa barci saboda PDP. Suna ta kakabawa jam’iyya kalubale iri-iri, amma Allah zai tabbatar mana da nasara. Mun tabbata, Allah mai adalci ne kuma baya goyon bayan zalunci”.
Ya kuma yi gargadi cewa wadanda ke tayar da rikici a jam’iyyar suna iya fuskantar hukunci, hukuncin aikinsu zai zo nan gaba.
A nasa jawabin, sabon shugaban NWC, Tanimu Turaki, ya yabawa kwamitin kan kokarin da suka yi. Ya kuma yi alkawarin cewa zai ci gaba da aiki tukuru don inganta cigaban PDP.