Delegates din jihata Rotimi Amaechi zasu zaba a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani da ke tafe a cewar gwamnan jihar Plateau

Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong, ya ce Delegates din Jam’iyar APC na Jihar zasu zabi Rotimi Amaechi, a matsayin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar a zaben fidda gwani da ke tafe.

Da yake jawabi ga Amaechi da Delegates na Jam’iyar APC a gidan Gwamnati da ke Jos a jiya, Gwamna Lalong, ya ce Rotimi Amaechi ya yiwa mutanen Jihar Alkhairai da yawa.

Gwamna Lalong ya ce ya koyi abubuwa da dama daga wurin Amaechi ta fannin shugabanci nagari.

A jawabinsa, Shugaban masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Hon Ibrahim Baba, ya ce Amaechi ya cancani zama shugaban kasa.

Tun farko a jawabin sa, Mista Rotimi Amaechi, ya ce zai samar da ayyukan yi ga Matasa da inganta fannin Lafiya, tare da inganta tsaro matukar ya zama shugaban kasa.

Comments (0)
Add Comment