Farfesa Osinbajo ya bayyana cewa sun dukufa wajen shirya matasan kasarnan domin fuskantar kalubalen shugabanci

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dukufa wajen shirya matasan kasarnan domin fuskantar kalubalen shugabancin kasarnan a gaba.

Osinbajo ya ce za a cimma hakan ne ta wasu tsare-tsare masu zaman kansu da na gwamnati na horar da shugabanni.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne jiya a Legas a wajen taron shekara-shekara na kungiyar darektoci na bana.

Shugaban ma’aikatan tarayya, Folashade Yemi-Esan ce ta wakilci mataimakin shugaban kasar a wajen taron.

Osinbajo ya ce taken taron abin yabawa ne domin yana haifar da tashi tsaye ga rashin makama a tsakanin matasa.

Ya ce bayanan da aka samu sun nuna cewa galibin ma’aikata suna tsakanin shekaru 20 zuwa 39 ne ta yadda hakan ya haifar da bukatar a yi wa matasa gyaran fuska tare da hadin gwiwa a dukkan bangarori.

Comments (0)
Add Comment