Guraren gyaran motoci a jihar Jigawa sun koka akan karancin ayyuka daga masu motoci

Hakan dai na faruwa ne yayin da farashin kayan gyaran motan ya ninka fiye da ninki biyu bayan cire tallafin man fetur wanda ba a taba ganin irinsa ba inda man ya tashi daga naira 200 zuwa naira 700.

A Dutse, babban birnin jihar Jigawa, masu motoci a yanzu suna amfani da motocin haya ne domin zirga-zirga saboda farashin man fetur ya karu sosai, wanda ya sa manyan tituna suka zama Fakai

Adamu Abubakar daya ne daga cikin masu sana’ar  anikancin mota a Dutse, ya ce yana da mata da ’ya’ya biyu amma abinci yana neman ya gagari iyalansa  saboda rashin samun aikin gyaran mota ya yi karanci. Adamu Abubakar ya ce kafin a cire tallafin suna samun ciniki sosai domin masu motoci a koda yaushe suna zuwa kawo musu gyara.

Comments (0)
Add Comment