Gwamna Badaru Abubakar ya amince da nadin Ado Yakubu Zandam a matsayin mataimaki na musamman ga gwamnan jiha akan zuba jari.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya amince da nadin Ado Yakubu Zandam a matsayin mataki na musamman ga gwamnan jiha akan zuba jari.

Kazalika, gwamnan ya amince da nadin Yushau Kafin Fulani a matsayin mataimaki na musamman ga gwamnan jiha kan ilmi matakin farko.

A sanarwar da sakataren gwamnatin jiha Adamu Abdulkadir Fanini ya bayar tace nadin ya fara aiki nan take.

Comments (0)
Add Comment