Gwamnan Jihar Zamfara ya rufe dukkan Kasuwannin da suke ci mako-mako a fadin Jihar saboda tsaro

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun, ya sanar da dokar rufe dukkan Kasuwannin da suke ci Mako-Mako a fadin Jihar a wani mataki na inganta lamuran tsaro da yake cigaba da tabarbarewa a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa Gwamna Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar Daliban Kwalegin Aikin Gona da Bakura wanda yan bindiga suka sake su bayan shafe kwanaki 12 a hannun su.

Gwamnan ya kuma, ce gwamnatin Jihar ta haramta sayar da Man fetur a bakin tituna, a wani mataki na hana kaiwa yan bindigar Man fetur.

Haka kuma, gwamnan Jihar ya haramta safarar Shanu da Itace a sassan jihar, inda ya kara da cewa dole ne a binciki masu safarar Abinci, domin tabbatar da cewa ba’a kaiwa yan bindigar ba.

Kazalika, Gwamnan ya bukaci mutanen Jihar su kai rahoton masu karya dokar da gwamnati ta shimfida.

Comments (0)
Add Comment