Gwamnan Nasir El-Rufai yayi bayanin dalilan da suka sanya aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnonin APC

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a jiya yayi bayanin dalilan da suka sanya aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnonin APC dangane da lokacin gudanar da babban taron kasa na jam’iyyar mai mulki.

Nasir El-Rufai ya sanar da haka bayan gwamnonin na APC sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin yi masa bayani dangane da matsalolin da ake fuskanta kafin babban taron.

A baya an shirya gudanar da babban taron a ranar Asabar mai zuwa amma kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar na kasa a ranar Litinin ya sanar da dage taron zuwa ranar 26 ga watan gobe na Maris.

Biyo bayan ganawa da shugaban kasa a jiya, Nasir El-Rufai ya amince cewa batun babban taron jam’iyyar ya raba kawunan gwamnonin APC.

Amma gwamnan na jihar Kaduna yace ba son zuciya bane ya haifar da rabuwar kawunan ba.

Comments (0)
Add Comment