Gwamnatin Buhari ce ta kara kudin makaranta na kwalejojin hadaka (FGC)

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta ce gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta sake duba sabon tsarin biyan kudin makaranta na kwalejojin hadin kai.

Hakan na kunshe ne a wasu takardu da aka samu daga ma’aikatar ilimi ta tarayya jiya a Abuja.

Takardun sun bayyana cewa sabon tsarin biyan kudin makaranta ya samu amincewar tsohon ministan ilimi, Adamu Adamu a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya daga ma’aikatar da ta so a sakaya sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN  jiya a Abuja cewa kudaden karatu a kwalejojin hadin kan gwamnati kyauta ne amma ana son dalibai su biya wasu abubuwa kamar kudin litattafai, Unifos da ciyarwa da kudin dakunan kwana.

Idan dai ba a manta ba a shekarar 2020 ne gwamnatin tarayya ta karbi Naira 15,000 a matsayin kudin kwana ga sabbin dalibai, wanda ya kawo adadin kudin zuwa N50,500.

Ta sake duba kudin zuwa N30,000 a watan Mayu, inda ta kawo jimlar kudin zuwa N100,000.

Sai dai kuma ga daliban da suka dawo, gwamnatin tarayya ta biya N48,500 a matsayin jimillar kudin a shekarar 2020 sabanin N47,000 a shekarar 2023 na daliban kwana. NAN

Comments (0)
Add Comment