Gwamnatin Jihar Jigawa ta ayyana ranar Litinin, 1 ga Muharram a matsayin ranar hutu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ayyana ranar Litinin, 1 ga Muharram, 1443 bayan Hijira, wadda ta yi daidai da 9 ga Agusta, 2021, a matsayin ranar hutu a jihar.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikata na Jiha Alhaji Hussaini Ali Kila, ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Dutse.

Sanarwar ta ce Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya bukaci ma’aikata da su yi amfani da ranar da babu aiki don yin addu’a ga kasa don kubutar da ita daga matsalolin tsaro.

Haka kuma sanarwar ta ce mutane suyi koyi da halayyar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SWA a lokacin hutun.

Gwamna Badaru Abubakar, ya kuma taya Musulmi murnar shigowar sabuwar shekarar Musuluncin, tare da yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki.

Sanarwar ta kara neman goyon baya da hadin kai na jama’a ga gwamnati yayin da take kokari don inganta muradansu duk da irin kalubalen da kasar ke fuskanta.

Tuni Jihohin Osun, Oyo, Kano, Sokoto, Kebbi and Jigawa suka shiga ba da hutu domin nuna murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci.

Comments (0)
Add Comment