Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadana, a wani mataki na rage al’umma da masu karamin karfi radadin da suke ciki

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadana, a wani mataki na rage Al’umma da masu karamin karfi radadin da suke ciki.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin a harabar kamfanin buga takardu mallakin Jihar Kano, Mukaddashin Gwamna Dr Nasiru Yusif Gawuna, ya bukaci mambobin kwamatin su kasance masu yin gaskiya da adalci a lokacin gudanar da ayyukan su.

Dr Gawuna, wanda ya yi jawabi kan muhimmancin ciyar da masu karamin karfi musamman a watan Ramadana, ya bukaci mutane suyi amfani da wannan dama.

Tun farko a jawabinsa, Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Karkokin Masarautu Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana cewa gwamnatin Jihar ta ware Naira Miliyan 550 domin gudanar da ciyarwar a cibiyoyi 140 wanda Jihar ta ware, kuma 8 a cikin birnin Kano suke.

Kwamishinan ya ce daga cikin kayayyakin da aka ware domin ciyarwar sun hada da Shinkafa, Wake, Fulawa, Gero, Man Girki da kuma Manja.

Comments (0)
Add Comment